Wasanni

Kotu ta soke hukuncin haramtawa City shiga gasar zakarun Turai

Kotun sauraron kararrakin wasanni ta duniya ta soke hukuncin haramtawa kungiyar Manchester City buga gasar cin kofin zakarun Turai tsawon shekaru 2.

'Yan wasan kungiyar Manchester City
'Yan wasan kungiyar Manchester City Reuters/Andrew Yates
Talla

Kotun ta kuma rage yawan tarar da a baya aka zartas City za ta biya kan saba ka’idar kashe kudade daga euro miliyan 30, zuwa euro miliyan 10.

A yau litinin kotun wasannin ta zartas da hukuncin, bayan zama kan daukaka karar da City ta yi kan hukuncin da hukumar wasannin kwallon kafa ta Turai UEFA ta yanke mata a watan fabarairun da ya gabata.

A waccan lokacin dai, hukuncin hukumar ta UEFA ya biyo samun kungiyar Manchester City da laifin karya ka’idojin kashe kudade fiye da samunta, abin da yasa ta haramta mata shiga gasar zakarun Turai tsawon shekaru 2 tare da cin ta tarar Euro milyan 30, hukuncin da kungiyar ta kalubalanta a gaban kotun sauraron kararrakin wasannin.

Tuni dai hukumar kwallon kafar Turai ta nuna rashin jin dadin soke hukuncinta kan City da kotun wasannin ta yi, abinda at danganta da rashin gamsuwar da alkalai suka yi da hujjojin da ta gabatar kan tuhumar kungiyar ta Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI