Wasanni

Milan ta shiga jerin kungiyoyin Turai masu zawarcin Osimhen

Wasan Najeriya dake kungiyar Lille a Faransa, Victor Osimhen.
Wasan Najeriya dake kungiyar Lille a Faransa, Victor Osimhen. AFP

AC Milan ta shiga sahun kungiyoyin kwallon kafar dake neman kulla yarjejeniyar da dan wasan gaba na Najeriya dake kungiyar Lille a Faransa Victor Osimhen.

Talla

Sai dai duk da bayanai sun ce Milan na shirin gabatar da tayi mai romo ga dan wasan, har yanzu takwararta a gasar Seria A wato kungiyar Napoli aka fi sa ran za ta samu nasarar daukar Osimhen mai shekaru 21.

A baya baya nan dan wasan da kungiyarsa ta Lille ke neman euro miliyan 60 kafin saida shi, yayi tattaki zuwa Italiya, inda ya gana da shugabannin kungiyar Napoli.

A yanzu haka dai, Osimhen na cikin matasan da suka yi fice a nahiyar Turai kan tamaula, wanda a kakar wasa ta bara ya ci wa Lille kwallaye 18 daga cikin wasanni 38 da ya buga mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.