Wasanni-Kwallon kafa

Maki biyu ya ragewa Real Madrid ta lashe La Liga

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan lashe kofin Spain.
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bayan lashe kofin Spain. REUTERS/Sergio Perez

Maki 2 cal ya ragewa Real Madrid ta Spain ta samu kafin iya bayyana ta a matsayin zakarar Laliga ta bana, bayan nasara kan Granada har gidanta da kwallaye 2 da 1 a daren jiya Litinin dai dai lokacin da ya rage wasanni biyu a kulle kaka.

Talla

Yayin wasan na jiya dai Ferland Mendy ne ya fara zurawa Madrid kwallonta na farko a minti na 10 gabanin Karim Benzema ya zura kwallo ta biyu a minti na 16, sai dai bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne Darwin Machis na Granada ya farke kwallo guda inda aka tashi wasa 2 da 1.

Bayan doka wasanni 36, Real Madrid din na matsayin jagora a teburin gasar ta Laliga da maki 83 tazarar maki 4 tsakaninta da babbar abokiyar dabinta Barcelona da ke matsayin ta 2 da maki 79.

Duk da kasancewar Real Madrid mafi lashe gasar ta Laliga har sau 33 a tarihi, za a iya cewa ta kwana biyu rabon da kofin gasar ya je gidanta domin kuwa tun a kakar wasa ta 2016 zuwa 2017 rabon da ta lashe yayinda a jere Barcelona da dage kofin gasar a kakar wasa ta 2017 zuwa 2018 da kuma kakar wasa ta 2018 zuwa 2019.

Matukar Madrid ta yi nasarar lallasa Villareal a wasan da za ta karbi bakoncita Alhamis din nan kai tsaye za ta zama zakarar bana karkashin gasar ta Laliga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.