Wasanni

Mourinho ya soki UEFA kan kayyade yawan kudin sayen 'yan wasa ga kungiyoyi

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Jose Mourinho ya ce lokaci ya yi da ya kamata a kawo karshen ka’idojin da UEFA ke gindaya wajen kashe kudin sayen ‘yan wasa a kowacce kaka.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham José Mourinho.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Tottenham José Mourinho. Reuters/Carl Recine/File Photo
Talla

Mourinho wanda ke wannan batu bayan nasarar Manchester City a kotun sauraron karakin zabe kan hukuncin dakatarwar shekaru 2 da UEFA ta yi mata a baya, ya ce ya jima yana kalubalantar dokokin na UEFA.

A Litinin din nan ne, kotun wasanni ta janye hukuncin UEFA na haramcin shiga gasar Turai har na 2 da ta gindaya kan Manchester City saboda rashin hujjojin da ke nuna kungiyar ta kashe kudin da ya wuce kima wajen sayen ‘yan wasa.

Manajojin Firimiya ciki har da Mourinho da takwaransa Jurgen Klopp na Liverpool sun jima suna caccakar dokokin na UEFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI