Wasanni

Rashford ya kusan zama dakta

Matashin dan wasa ga na Manchester United Marcus Rashford zai zama mutun mafi karancin shekaru da ya karbi shaidar digirin ban-girma daga jami’ar Manchester.

Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford
Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford REUTERS/Phil Noble
Talla

Rashford mai shekaru 22 zai samu wannan daukakar ce saboda gwagwarmayarsa kan yaki da matsalar talauci da ke addabar kananan yara.

Dan wasan na yin gwagwarmaya don ganin gwamnati ta bai wa kananan yara  kimanin miliyan 1 da dubu 300 katin karbar abinci kyauta a yayin hutun kaka a Ingila.

Wannan digirin ban-girman shi ne daraja mafi kololuwa da jami’ar ta Manchester United ke bayarwa.

Dan wasan ya ce, wannan lambar girma abin alfahari ne a gare shi da iyalinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI