Arsenal ta hana Liverpool kafa sabon tarihi
Arsenal ta kawo karshen kudirin Liverpool na kafa sabon tarihin bajintar samun maki fiye da 100 a gasar Firimiyar Ingila bayan ta doke ta da ci 2-1 a daren Laraba.
Wallafawa ranar:
Tawagar ta Jurgen Klopp na bukatar lashe dukkannin wasanni 3 da suka rage a gasar ta wannan kaka don shafe tarihin da Manchester City ta kafa na maki 100 a gasar kaka ta 2018.
Sadio Mane ya dora Liverpool a kan hanyar cimma wannan buri bayan da ya antaya kwallon da Andrew Robertson ya kawo mai daga kusurwa a ragar Arsenal.
Amma wasu kurakurai daga Liverpool din sun kawo mata cikas, lamarin da ya sa ta samu rashin nasara na 3 a wannan kaka.
Wani mayar da kwallo baya da mai tsaron bayan Liverpool Virgil van Dijk ya yi da babu azanci a ciki ne ya shiga kafar Alexandre Lacazette kai tsaye, shi ko ya zabga ta a ragar Liverpool a cikin minti na 32.
Mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker shi ma ya tafka wani kuskure, wanda ya sake baiwa Lacazatte damar saka kwallo ta biyu a ragar Liverpool.
Tun da Liverpool ta karbi kofin Firimiyar Ingila na wannan kaka, ta kasa lashe wasanni 3 cikin wasanni 5 da suka rage mata.
Yanzu Liverpool na da maki 93, da saura wasanni 2 kacal da suka rage, kuma maki 99 ne za ta iya kaiwa ko da ta lashe dukkannin wasanni biyun.
Yanzu Arsenal na matsayiu na 9 a wannan gasa ta Firimiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu