Wasanni-Kwallon kafa

Babu siddabarun da zai ceto Arsenal sai ta sayi manyan 'yan wasa-Arteta

'Yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar da ta lashe kofin Community Shield.
'Yan wasan Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a shekarar da ta lashe kofin Community Shield. Reuters / Andrew Couldridge

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce babu wani siddabaru da zai iya aiwatarwa don yin takara da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a kaka mai zuwa idan har mahunkuntar kungiyar ba su fidda kudi sun sayi manyan ‘yan wasa ba.

Talla

Arteta ya yi wannan bayanin ne bayan da tawagarsa ta doke zakarun gasar Firimiyar Ingilar da ci 2 da 1 a daren jiya Laraba.

Duk da cewa Liverpool ta yi rashin nasara a hannun Arsenal wanda shine rashin nasararta karo na 3 a wannan kaka, Liverpool ta baiwa Arsenal, wacce ke a matsayi na 9 tazarar maki 40.

Arsenal na kan hanyar kammala gasar Firimiyar Ingila a matsayi mafi kaskanci da ta tsinci kanta tun a kakar wasa ta 1994/95.

Arteta ya tada kafadar wannan tawaga ta ‘yan wasan Arsenal tun da ya kama aikin horar da ita a watan Disamba, kuma ya ce ya yi na’am da irin kwazon ‘yan wasansa.

Sai dai abu ne mai kamar wuya a baiwa Arteta kudade masu yawa don sayen ‘yan wasa a kaka mai zuwa duba da cewa ba za a dama da kungiyar a gasar zakarun nahiyar Turai a kaka mai zuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.