Wasanni-Kwallon kafa

Martins ya maye gurbin Ighalo a Shenhua

Kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua ta kammala sayen tsohon dan wasan Najeriya da kuma Inter Milan Obafemi Martins, wanda ya yi wa kungiyar kome, bayan da ya kasance a cikinta a tsakanin shekara ta 2016 da 2018.

Obafemi Martins
Obafemi Martins Reuters
Talla

Dan shekara 35 din ya koma kungiyar ne a wannan karo don ya maye gurbin Odion Ighalo, wanda aka tsawaita zamansa a matsayin aro a Manchester United ta Ingila zuwa shekara ta 2021.

A ranar Laraba, Martins ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram sanye da rigar kungiyar ta Shenhua tare da sauran ‘yan wasan tawagar, kuma wani na kusa da shi dan wasan ya tabbatar wa da manema labarai cewa lallai ya yi wa kungiyar kome.

Bayan da ya bar Seattle Sounders a shekarar 2015 zuwa shenhua, Martins ya ci mata kwallaye 32 daga wasanni 59 a dukkan gasanni, kafin u yi hannun riga shekarar 2018.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI