Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon tare da Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna ne kan nasarar da dan Najeriyar nan, Kamaru Usman ya samu a babbar gasar damben zamani da aka gudanar a Amurka. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa dan wasan saboda bajintar da ya nuna. Kazalika shirin ya yi nazari kan kalubalen da ke gaban Real Madrid bayan ta lashe kofin La Liga karo na 34 a Spain.
Sauran kashi-kashi
-
Wasanni Bahaushiya Mace ta farko da ke horar da 'yan wasan kwallon kafa Maza Shirin Duniyar wasanni tare da Khamis Saleh a wannan mako ya leka garin Mai Tsidau ne a Karamar hukumar Makodan Jihar Kano ta arewacin Najeriya, dan kawo muku yadda wata baiwar Allah mai suna Coach Fatima, wadda ta zamo mace daya tilo da ke horas da kungiyar kwallon kafa ta maza, wadda zancen nan da ake tuni labarinta ya karade kafafen sada zumunta a Najeriya.15/05/2023 09:59
-
Wasanni Halin da tsoffin 'yan wasan kwallon kafar Najeriya ke ciki Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya maida hankali ne kan halin kunci da wasu tsoffin 'yan wasan kwallon kafar Super Eagles ta Najeriya da suka wakilci kasar a matakai daban-daban ke ciki.24/04/2023 10:00
-
Wasanni Duniyar Wasanni: Tarihin Mesut Ozil tsohon dan wasan Jamus Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan mako tare da Khamis Saleh ya duba tarihin tsohon dan wasan tawagar kasar Jamus da ya yi murabus daga buga kwallon kafa a ‘yan kwanakin nan wato Mesut Ozil.10/04/2023 09:58
-
Wasanni Yadda ake ci gaba da fafata gasar Super League din kasar Niger Shirin "Duniyar Wassani" na wannan makon ya leka ne Jamhuriyar Nijar inda ake ci gaba da fafatawa a gasar lik din kasar.An kammala wasan zagaye na farko a gasar lik din Jamhuriyar Niger, da kungiyoyi 14 ke fafatawa a cikin ta.Gasar ta bana ta fuskanci tsaiko da dama ganin yadda a tsakayar ta aka tafi hutu don halartar gasar CHAN, sannan kuma aka sake bada hutu ga 'yan wasa bayan kammala gasar.13/03/2023 09:57
-
Wasanni Yadda gasar Firimiyar Ghana BETPAWA ke samun koma baya Shirin mu na wannan makon zai yi duba ne akan gasar firimiyar kasar Ghana wacce ake wa lakabi da BETPAWA. A yanzu gasar ba ta cikin jerin gasannin 10 na farko a Afrika, lamarin da ya nuna irin kalubelen da ta ke fuskanta, wanda suka hada da rashin halartan filin wasa daga magoya bayan kungiyoyi da rashin masu saka hanun jari da dai sauransu .06/03/2023 10:00