Wasanni-Kwallon kafa

Klopp ya lashe kyautar gwarzon koci a Ingila

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ne ya lashe kyautar gwarzon mai horarwa a gasar Firimiyar Ingila, kyautar da kungiyar masu horarwa ta gasar ke bayarwa duk shekara.

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp.
Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp. Reuters
Talla

Tawagar Klopp ta lashe kofin gasar Firimiya a bana, a karon farko cikin shekaru 30.

A bangaren masu horar da mata ‘yan wasan tamola kuwa, Emma Hayes ne ya lashe wannan kyauta, bayan da ya jagoranci tawagar mata ta kungiyar Chelsea zuwa ga lashe kofin kalubale na mata a wannan kaka.

A bangaren gasar da ke bi da Firimiya kuwa, wato Championship, kocin Leeds United Marcelo Bielsa ne ya ci wannan kyauta, sakamakon jagorantar tawagarsa zuwa samun shiga gasar Firimiyar Ingila.

Da yake sanar da kocin da ya lashe kyautar gwarzon mai horarwa a gasar Firimiyar Ingila ta tashar Sky Sports, tsohon kocin Manchester United Sir Alex ya ce lallai Klopp ya cancanci kyautar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI