Wasanni-Kwallon kafa

Mbappe zai yi jinyar makonni uku

Dan wasan gaba na Paris St-Germain Kylian Mbappe wanda ke fama da rauni a kafarsa ba zai samu fafatawa a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar zakarun nahiyar Turai tsakanin kungiyarsa da Atalanta a birnin Lisbon ranar 12 Agusta ba.

Kylian Mbappé dan wasan gaba na PSG, lokacin da aka rafke shi a wasan PSG da Saint Etienne.
Kylian Mbappé dan wasan gaba na PSG, lokacin da aka rafke shi a wasan PSG da Saint Etienne. FRANCK FIFE / AFP
Talla

Mbappe, mai shekaru 21, ya samu rauni a idon sawunsa ne a yayin wasan karshe na kofin kalubalen Farasansa da PSG ta kara da Saint-Etienne a ranar Juma’ar da ta gabata, lamarin da ya sa zai shafe makonni 3 ba tare da ya murza leda ba.

Sai dai yana iya dawowa a wasaa kusa da na karshe idan har kungiyar ta sa ta samu nasarar tsallakewa.

Dan wasan na kasar Faransa ya fita daga filin wasa yana hawaye bayan da dan wasan baya na Saint-Etienne Loic Perrin ya rafke shi kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Sakamakon tsaikon da annobar coronavirus ta janyo a kowane fanni na rayuwa har ma da wasannin kwallon kafa, karkare gasar zakarun nahiyar Turai ta bana zai hada ne da fafatawa irin ta sili daya kwale tsakanin tawagogi 8 da za a yi a Lisbon babban birnin Portugal, ana kuma sa ran buga wasan karshe a ranar 23 ga watan Agusta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI