Arthur ya kauracewa atasaye da Barcelona
Kungiyar Barcelona dake gasar La Liga a Spain, ka iya hukunta dan wasanta Arthur Melo dan kasar Brazil, sakamakon kauracewa halartar atasayen da yayi a baya bayan nan.
Wallafawa ranar:
Wata guda da ya gabata, kungiyar ta Barcelona ta saida dan wasan nata Arthur ga Juventus kan euro miliyan 72, inda kuma ta sayi dan wasan tsakiya na kungiyar ta Juventus Miralem Pjanic. Sai dai sauyin shekar ‘yan wasan ba za ta tabbata ba, sai a karshen kakar wasa ta bana.
Tun bayan shelar matakin saida shi ga Juventus a ranar 29 ga watan Yuni, Arthur bai sake haskawa a wasannin Barcelona ba, a baya bayan nan ne kuma ya dauki matakin soma kauracewa halartar atasaye tare da takwarorinsa a kungiyar.
Ranar Talata 28 ga watan Yuli, bayan gajeren hutun kammala gasar La Liga, ‘yan wasan Barcelona suka koma atasayen tunkarar fafatawarsu da Napoli cikin watan Agusta, a gasar cin kofin zakarun Turai zagayen kungiyoyi 16.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu