Wasanni-Kwallon kafa

Infantino zai gurfana gaban kuliya

Shugaban FIFA, Gianni Infantino.
Shugaban FIFA, Gianni Infantino. Attila KISBENEDEK / AFP

Masu gabatar da kara a Switzerland sun shigar da karar shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, Gianni Infantino a gaban kotu.

Talla

Matakin na su na da nasaba ne da wata ganawar sirri da ake zargin Infantino ya yi da attorney janar na Swiszerland Michael Lauber.

A makon da ya gabata, Lauber ya bayyana aniyar yin murabus bayan wata kotu ta ce ya yi rufa rufa a game da ganawar, kuma ya shirga karya ga masu bincike a kan jerin badakalar da suka shafi hukumar FIFA.

Dukkannin su sun musanta aikata ba daidai ba.

Wannan na zuwa ne bayan da aka nada mai gabatar da kara na musamman Stefan Keller a watan da ya gabata don ya yi bitar korafe korfen da aka yi a kan mutanen biyu.

Hukumar da ke sa ido a kan ayyukan ofishin attorney janar din ta ce mai binciken ya ga alamun aikata ba daidai ba a game da ganawar Infantino da Lauber, kuma zai gurfanar da su gaban kuliya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.