Wasanni-Kwallon kafa

Kamfanin Saudiyya ya janye daga cinikin sayen New Castle

Kamfanin da ya so sayen kungiyar kwallon ta New Castle United dake Ingila ya janye daga maganar ana tsakar ciniki sakamakon tsaiko da dogon turanci da aka yi ta yi.

wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta Ingila.
wasu daga cikin 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Newcastle United ta Ingila. Reuters
Talla

Wakilan kamfanin, karkashin jagorancin hukumar zuba jari ta kasar Saudi Arabia sun kada takalmansu sun fice daga zauren cinikin hankalinsu a tashe.

Wannan ciniki da aka ce ya kai fam miliyan 300 wanda hukumar da yerima bin Salman na Saudiyya ke jagoranta, ya janye daga cininikinsa ne saboda tsawon lokacin da aka bata ba a cimma matsaya ba.

A wata sanarwa, kamfanin ya jinjina wa kungiyar bisa niyyar da ta nuna na yin ciniki da shi, amma kuma ya ce ya kai makura, ba zai ci gaba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI