Wasanni

Osimhen ya sauya sheka daga Lille zuwa Napoli

Kungiyar Napoli dake gasar Seria A a Italiya ta sanar da kulla yarjejeniya da matashin dan wasan Najeriya Victor Osimhen daga kungiyar Lille dake gasar Ligue 1 a Faransa.

Victor Osimhen dan wasan Najeriya da ya sauya sheka daga kungiyar Lille dake Faransa, zuwa Napoli a Italiya.
Victor Osimhen dan wasan Najeriya da ya sauya sheka daga kungiyar Lille dake Faransa, zuwa Napoli a Italiya. AFP/JEAN-FRANCOIS MONIER
Talla

Dukkanin kungiyoyin na Napoli da Lille sun tabbatar da sauyin shekar dan wasan ta shafukansu na Twitter a yau Juma’a, bayan cimma yarjejeniya cinikin da Napoli ta biya euro miliyan 81.

Tuni dai kungiyar ta Napoli ta baiwa Osimhen riga mai lamba 9.

Dan wasan dai na sahun gaba cikin jerin zakakuran masu nasibin sarrafa kwallo a tsakanin matasan ‘yan wasa a nahiyar Turai, inda yake a matsayin mai daraja ta 3 a gasar Ligue ta Faransa kafin sauyin shekar da yayi.

Osimhen mai shekaru 21, ya kafa tarihin zama dan wasa mafi tsada daga Najeriya a duniyar kwallon kafa, zalika a halin yanzu, shi ne dan wasa mafi tsada da kungiyar Napoli ta taba saye a tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI