Wasanni

Rashin kudi ya hana Barcelona sayo Neymar

Dan wasan PSG, Neymar
Dan wasan PSG, Neymar FRANCK FIFE / AFP

Shugaban Barcelona Josep Maria Batomeau ya ce, abu ne mai matukar wahala ga kungiyar ta sake sayo Neyrmar daga PSG a daidai wannan lokaci da ake fama da matsalar tattalin arziki saboda annobar coronavirus.

Talla

Kazalika wannan matsalar ta shafi cuku-cukun da Barcelona ke yi na dauko dan wasan gaba na Inter Milan wato, Lautaro Martinez.

A yayin zanta wa da manema labarai a Spain, shugaban na Barcelona ya ce, kungiyar ta samu ribar Euro miliyan 200, kasa da abin da ta kiyasta samu tsakanin watan Maris da Yuni saboda wannan annobar ta Covid-19.

A watan Agustan shekara ta 2017 ne, PSG ta Faransa ta sayo Neymar daga Barcelona akan farashi mai tsada har Euro miliyan 222, amma a yanzu, kungiyar na fatar dawo da tsohon dan wasan nata a cikin wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI