Isa ga babban shafi
Wasanni

Chelsea za ta sallami 'yan wasa 9

N'Golo Kante daya daga cikin 'yan wasa 9 da Chelsea ke shirin sallama
N'Golo Kante daya daga cikin 'yan wasa 9 da Chelsea ke shirin sallama Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 1

Kungiyar Chelsea ta bayyana aniyar saida ‘yan wasanta akalla 9, da zarar an bude kasuwar musaya ko cinikin ‘yan wasa, don kara karfi a sabuwar kakar wasan dake tafe.

Talla

‘Yan wasan da Chelsean za ta saida sun hada da, Ross Barkley mai fama da rauni, Bakayoko dake zaman aro a Monaco, Zouma, Marcos Alonso, Andreas Christensen, Emerson Palmieri da kuma N’Golo Kante, wanda a kakar wasa ta bana, wasanni 23 kawai aka soma da shi.

Sauran ‘yan wasan sun ne Michy Batshuayi da kuma Kepa Arrizabalaga.

Tuni dai kungiyar ta Chelsea ta sayi ‘yan wasa 2 da suka hada da Hakeem Ziyech daga Ajax da kuma Timo Werner daga RB Leipzig.

A ranar 1 ga watan Agusta Chelsea ta sha kaye a hannun Arsenal da kwallaye 2-1, yayin wasan karshe na gasar cin kofin FA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.