Wasanni

Mai yiwuwa Barcelona ta kulla yarejejniya da tsohon kocin Tottenham

Tsohon mai horas da kungiyar Tottenham Mauricio Pochettino
Tsohon mai horas da kungiyar Tottenham Mauricio Pochettino Reuters / Hannah McKay Livepic

Mai yiwuwa kungiyar Barcelona ta kulla yarjejeniya da tsohon mai horas da Tottenham Mauricio Pochettino a sabuwar kakar wasa.

Talla

Kwararan majiyoyi daga Spain kamar yadda jaridar 'Daily Mail' ta ruwaito, sun ce a halin yanzu shugabannin kungiyar ta Barcelona sun bayyana Pochettino a matsayin koci na farko da suke son maye gurbin mai ci Quique Setien.

Batun maye gurbin Setien da tsohon kocin Tottenham ya karfafa ne a makwannin baya bayan nan, sakamakon gaza jagorantar Barcelona da yayi wajen lashe kofin gasar La Liga.

Kafin Barcelona, kungiyoyin da suka nemi kulla yarjejeniya da Mauricio Pochettino a baya sun hada da Juventus, Monaco da kuma Newcastle United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.