Wasanni

Sanchez ya amince da yarjejeniyar dindindin da Inter Milan

Alexis Sanchez
Alexis Sanchez Reuters

Inter Milan ta cimma yarjejeniya da Manchester United kan kulla yarjejeniya da Alexis Sanchez, dan wasan na United da a yanzu haka ke tare da kungiyar ta Inter a matsayin aro.

Talla

Yanzu haka haka dai Sanchez mai shekaru 31, ya shafe kakar wasa guda kenan a gasar Seria A ta Italiya, bayan mika shi aro da Manchester United ta yi.

Mujallar 'Corriera della Sera' dake Italiya ta ruwaito cewar Inter Milan da United sun amince da fam miliyan 13 da dubu 500 a matsayin kudin sauyin shekar Alexis Sanchez, wanda zai shafe shekaru uku nan gaba tare da kungiyar ta Inter.

A baya dai dan wasan na karbar albashin dubu 400 ne duk mako a Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.