Wasanni

Real Madrid ta ajiye Bale a wasanta da Manchester City

Gareth Bale
Gareth Bale REUTERS/Javier Barbancho

Kungiyar Real Madrid ta cire Gareth Bale daga cikin tawagarta ta ‘yan wasa 24 da za ta fafata da Manchester City a ranar Juma’a a gasar zakarun Turai, matakin kungiyoyi 16 zagaye na biyu.

Talla

Bale mai shekaru 31 ya buga wa Real Madrid wasanni biyu daga cikin wasani 11 tun bayan da kungiyar ta koma fagen taka leda a cikin watan Yuni a Spain.

Tun a cikin watan Satumban shekarar 2013, Bale ya koma Real Madrid daga Tottenham a kan farashin Pam miliyan 85, kuma ya taimaka wa kungiyar wajen lashe kofin gasar zakarun Turai har sau hudu.

A bangare guda, Real Madrid na fuskantar barazana a wasan na gobe, lura da cewa, Manchester City dai ta samu nasara a kanta da ci 2-1 a haduwarsu ta zagayen farko a cikin watan Fabairu kafin tafiya hutun dole na coronaviurus har kusan watanni biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.