Wasanni-Kwallon kafa

Bayern Munich za ta sayar da Alcantara - Rummenigge

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Bayern Karl-Heinz Rummenigge ya ce lallai kungiyar za ta sayar da dan wasanta Thiago Alcantara idan har aka taya shi da daraja.

Dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara.
Dan wasan Bayern Munich Thiago Alcantara. REUTERS/Eloy Alonso
Talla

Saura shekara guda kwantiragin Thiago ya kare a kungiyar, kuma an sha danganta shi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a watannin baya.

A watan Yuli Rummenigge ya tabbatar da cewa dan wasan mi shekaru 29 ya ki amincewa da sabanta kwantiraginsa da kungiyar, sakamakon bukartar da yake da ita ta gwada basirarsa a wata kasa banda Jamus.

Wannan labari dai ya karfafa wa Liverpool gwiwa a yunkurin da take na dauko dan wasan.

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya dade da cewa yana matukar sha’awar dan wasan na kasar Spain, sai dai har yanzu Bayern Munich ba ta ba da sanarwar tayi daga wata kungiya, kan dan wasan  da ake hasashen darajarsa ta kai fam miliyan 35.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI