Wasanni

Akwai jan aiki a gaban Messi a wasansu da Bayern

Lionel Messi
Lionel Messi REUTERS/Sergio Perez

Akwai jan aiki a gaban Lionel Messi na Barcelona dangane da samar wa kungiyarsa gurbi a matakin wasan dab da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai.

Talla

A gobe Juma’a ne Barcelona za ta kece raini da Bayern Munich a Lisbon, wasan da ake kallo a matsayin karan-batta, lura da cewa, kungiyoyin biyu na rike da kambin gasar zakarun Turai har guda biyar-biyar kowacce daga cikinsu.

Kofin La Liga ya subuce wa Barcelona, bayan Real Madrid ta dage kofin a bana, yayin da a yanzu kungiyar ke hararar kofin zakarun Turai.

Barcelona ta dogara kacokan kan Messi mai shekaru 33 a wasan da za ta yi da Bayern Munich wadda ba kanwar-lasa ba ce.

Kodayake Messi ya jefa kwallaye biyu a wasan da Barcelona ta doke Bayern Munich a shekarar 2009 a matakin kwata fainal a gasar zakarun Turai, inda a wanan lokacin ma, Barcelona ta lashe kofin gasar karkashin jagorancin Pep Guardiola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI