PSG ta tsallake rijiya da baya a gasar zakarun Turai
Wallafawa ranar:
A karon farko cikin shekaru 25, PSG ta Faransa ta samu gurbi a matakin wasan dab da na karshe na gasar cin kofin zakarun Turai bayan ta doke Atalanta da kwallaye 2-1 a karawar da suka yi a ranar Laraba a Lisbon.
Jim kadan da samun wannan nasarar, dan wasa mafi tsada a duniya wato Neymar ya bayyana cewa, da ma bai taba tunanin cewa za su koma gida ba, kuma ba su karaya ba, yayin da kocin kungiyar Thomas Tuchel ya ce, da farko ya zaci cewa, za a yi waje da su a gasar bayan sun shafe tsawon minti 88 Atalanta na jan ragama da ci 1-0 kafin daga bisani Marquinhos da Choupo-Moting su jefa kwallaye biyu a mintina na 90 da kuma 93.
Neymar da Mbappe ne suka jajirce har suka tabbatar cewa, PSG ta samu gurbin a matakin wasan dab da na karshe.
Yanzu haka PSG za ta hadu da ko dai RB Leipzig ko kuma Atletico Madrid a ranar Talata mai zuwa a matakin wasan dab da na karshe na gasar.
A yammacin wannan Alhamis ne za a kece raini tsakanin RB Leipzig da Atletico Madrid a Estadio Jose Alvalade.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu