Jaridun Spain sun yiwa Barcelona raddi kan abin kunyar da ta yi a gasar zakarun Turai

'Yan wasan Barcelona Luis Suarez da Lionel Messi yayin jimamin mummunan kayen da suka sha a hannun takwarorinsu na Bayern Munich
'Yan wasan Barcelona Luis Suarez da Lionel Messi yayin jimamin mummunan kayen da suka sha a hannun takwarorinsu na Bayern Munich Reuters

Jaridun kasar Spain sun yiwa kungiyar Barcelona raddi sakamakon wulakancin da kungiyar Bayern Munich tayi musu a gasar cin kofin zakarun Turai da ya gudana daren jiya wanda suka bayyana a matsayin ‘abin kunya’ da kuma ‘wulakanci’.

Talla

Manyan Jaridun kasar da suka hada da Marca da AS da Sport da kuma Mundo Deportivo sun ce sakamakon wasan daren jiya da ya nuna yadda Bayern ta murkushe Barcelona da ci 8-2 ya kawo karshen jagorancin watanni 7 da Quique Setien ke yi a kungiyar, wanda shine rashin nasara mafi muni da Barcelona ta gani a gasar Turai, inda suka bayyana tsohon manajan kungiyar Tottenham Mauricio Pochettino a matsayin wanda yake sahun gaba wajen maye gurbinsa.

Jaridar Marca ta buga ‘Abin Kunya’ a shafin ta na farko tare da hotunan Luiz Suarez da Lionel Messi suna nadamar abinda ya faru a shafin farko, yayin da Jaridar tace yanzu haka Setien ya jefa kafar sa daya da rabi a wajen kungiyar, inda tace a karon farko a cikin shekaru 13 za a je wasan kusan da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai ba tare da kungiyar Spain koda guda ba.

Jaridar AS ta buga hotan Lionel Messi a shafin farko ya rufe baki da hancin sa, inda ta yiwa labarin take ‘Abin kunyar tarihi’, inda take cewa dukar da Bayern ta yiwa Barcelona ya shafi kowanne bangare na kungiyar, yayin da Jaridar Sport tace an kunyata kungiyar Barcelona dake da kofunan Turai 5.

Jaridar Mundo Deportivo ta bayyana rashin nasarar Barcelona a matsayin kawo karshen karni ga kungiyar da kuma raba gari da manaja Setien, yayin da ta wallafa hotan Gerard Pique na share fuskar sa.

Daukacin Jaridun sun wallafa kalaman Gerard Pique na kiran kawo sauyi a kungiyar yayin da shugaba Josep Maria Bartomeu ya sha alwashin yin haka.

Jaridar tace yanzu haka Pochettino wanda tun a watan Nuwambar bara ya rasa aikin sa a Spurs da kuma wani tsohon manajan kungiyar Espanyol na sahun gaba wajen maye gurbin Setien.

Rahotanni sun ce tsohon dan was an kungiyar Xavi dake horar da kungiyar Al Sadd dake Qatar da kuma Ronald Koeman na cikin wadanda ake saran su nemi jagorancin kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.