Wasanni-Kwallon kafa

Mai yiwuwa na yi bankwana da Tamaula a 2024- Jurgen Klopp

Jurgen Klopp mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool.
Jurgen Klopp mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool. REUTERS/Charles Platiau

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce da yiwuwar ya juya baya ga tamaula bayan karewar wa’adinsa na horar da Club din a 2024.

Talla

Klopp mai shekaru 53 ko a lokacin karewar kwantiraginsa da Borussia Dortmund cikin shekarar 2015 sai da ya bukaci hutun shekara guda gabanin komawa fagen tamaula amma Liverpool ta matsa lambar da ya kaishi ga rattaba hannu kan kwantiragin horar da ‘yan wasanta don maye gurbin Brendan Rodgers.

A cewar Klopp yayin zantawarsa da jaridar wasanni ta Sportsbuzzer a Jamus, yana bukatar hutun shekara guda bayan karewar wa’adin inda daga nan ne kuma zai tambayi kansa ko yana bukatar ci gaba da tamaula ko kuma akasin haka.

Cikin kalaman na Klopp ya ce matukar ya tabbata zuciyarsa ta karkata ga yin wani abu na daban ko shakka babu zai yi bankwana da tamaula.

Tun bayan karbar ragamar horar da Liverpool a 2015, Jurgen Klopp ya yi nasarar kai Club ding a nasarar dage kofin zakarun Turai a 2019, kana zakarar duniya a bana tukuni nasara mafi kayatarwa ta dage kofin Firimiya karon farko cikin shekaru 30.

Ko a kakar 2019 Jurgen Klopp ne ya lashe kayautar gwarzon mai horar ta duniya yayinda 'yan wasansa suka fi na kowacce kungiya yawa a jerin wadanda suka shiga sahun lashe kyautar Ballon d'Or.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.