Wasanni-Kwallon kafa

Vincent Company ya karbi ragamar horar da kungiyar Anderlecht

Tsohon dan wasan Manchester City Vincent Kompany
Tsohon dan wasan Manchester City Vincent Kompany Photo: Reuters/Jason Cairnduff

Tsohon Kaftin din Manchester City Vincent Company ya amince da kwantiragin shekaru 4 don horar da kungiyar kwallon kafa ta Anderlecht matakin da ke zuwa bayan rataye takalminsa yau litinin.

Talla

Tun a bara Company mai shekaru 34 ya sauya sheka daga Manchester City zuwa Club din na Belgium kungiyar da ya faro kwallonsa tun yana yaro, amma kwantiragin na bara a matsayin dan wasa kuma mai taimakawa mai horarwa, inda wani lokacin ya ke taka leda wani lokacin kuma ya taimakawa Franky Vercauteren wanda ke matsayin Kocin Anderlecht a baran.

A yau ne dai kungiyar ta Anderlecht ta sanar da nadin na Company a matsayin shugaban tawagar masu horar da Club din don maye gurbin Franky.

Cikin kalamansa bayan rattaba hannu kan kwantiragin a matsayin Koci, Company ya ce yana fatan kai Club din ga gagarumar nasara a matsayinsa na Koci dalili kenan da ya sanyashi rataye takalminsa.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ce farkon taya tsohon Kaftin din na ta murnar sabon mukamin kana fitattun ‘yan wasa ciki har da Romelu Lukaku.

Company wanda ya taka ledawa Belgium har sau 89, a matakin kasa ya dage kofin Begium 2 a matakin kungiyoyi kuma ya yi nasarar dage kofin Firimiya har sau 4 kana kofin FA 2 tukuna lig 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.