Wasanni

Koeman ya amince da karbar aikin horas da Barcelona

Ronald Koeman
Ronald Koeman Reuters / Darren Staples Livepic

Wani lokaci nan gaba kadan ake sa ran Barcelona ta bayyana tsohon dan wasanta Ronald Koeman a matsayin sabon kocinta, don maye gurbin Quique Setien da ta kora.

Talla

Kafar yada labaran wasanni ta Sky Sports ta ruwaito cewar, bayan tattaunawa da wakilan Barcelona, Ronald Koeman dake horas da tawagar kwallon kafar kasar Netherlands ya amince da karbar ragamar jagorantar kungiyar ta Barcelona.

Hukumar gudanarwar kungiyar ta Barcelona ta yanke hukuncin sallamar tsohon kocinta Quique Setien a ranar litinin ne, bayan shafe akalla sa’o’i 6, tana taro kan makomar kungiyar, sakamakon lallasa ta da kwallaye 8-2 da Bayern Munich tayi a wasan kwata final na gasar zakarun Turai.

A watan janairun da ya gabata, Barcelon ta kulla yarjejeniya da Setien, sai dai hakarsu ba ta cimma ruwa ba a kakar wasan da ta kare, biyo bayan rasa kofin gasar La Liga da suka yi, da kuma mummunan kayen da suka sha na ficewa daga gasar Zakarun Turai.

A wani matakin kuma, shugabannin kungiyar ta Barcelona sun bayyana 15 ga watan Maris na shekara mai zuwa a matsayin ranar zaben sabon shugaba, a maimakon cikin watan Yuni da aka tsara zaben zai gudana.

Zalika yayin taron na jiya Barcelonan ta kuma cimma matsayar sake yunkurin maido da dan wasanta Neymar da ta saidawa PSG, inda ta ce a shirye take ta mikawa kungiyar ta PSG dan wasanta Antoine Griezman da karin fam miliyan 55.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.