Wasanni

Barcelona ta nada sabon koci

Ronald Koeman
Ronald Koeman Reuters/Phil Noble

Barcelona ta nada tsohon dan wasanta, Ronald Koeman a matsayin sabon kocinta kamar yadda shugaban kungiyar Josep Maria Bartomeu ya sanar.

Talla

Bartomeu ya ce, Koeman zai kasance kocin Barcelona a kaka mai zuwa.

Koeaman wanda ke jagorancin tawagar kwallon kafar Netherlands tun shekarar 2018, ya maye gurbin Quique Setien wanda Barcelona ta raba gari da shi bayan Bayern Munich ta yi mata zazzagar kwallaye 8-2 a matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar zakarun Turai a makon jiya.

A daren jiya ne, dillalin Koeman da mahukuntan Barcelona suka yi zaman tattaunawa game da bai wa kocin kwantiragin shekaru biyu a tashin farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.