Wasanni-Kwallon kafa

Dan takarar shugabancin Barcelona ya sha alwashin korar sabon kocinsu

Wasu 'yan wasan Barcelona.
Wasu 'yan wasan Barcelona. Reuters

Dan takarar shugabancin kungiyara kwallon kafa ta Barcelona, Victor Font, ya sha alwashin korar sabon kocin da kungiyar ta nada, Ronald Koeman, don maye gurbinsa da tsohon dan wasan kungiyar, Xavi Hernandez.

Talla

A Talatan nan aka kaddamar da Koeman a matsayin koci a Camp Nou, biyo bayan sallamar Quique Setien.

Shugaban kungiyar mai ci, Josep Maria Bartomeu yana cikin matsin lamba, a daidai lokacin da aka shirya tsaf don gudanar da zabe a ranar 15 ga watan Maris ta shekarar 2021.

Font na takara ne don maye gurbin Bartomeu, wanda ke kan ragamar tafiyar da kungiyar tun a shekarar 2014.

A wata ganawa da aka yi da shi ta wata tashar talabijin, Font ya ce zai kori Koeman ko da kuwa ya yi kokari, saboda Xavi ya fahimci irin kwaskwarimar da ake bukata a kungiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.