Wasanni-Kwallon kafa

Lashe Laligar bana ya fi mun komai - Zidane

Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane.
Mai horas da kungiyar Real Madrid Zinedine Zidane. REUTERS/Juan Medina

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce jagorantar kungiyar zuwa lashe gasar kofin Laliga duk da tsaikon da annobar coronavirus ta janyo abin alfahari ne a gareshi.

Talla

Shahararren tsohon dan wasan Faransan mai shekaru 48 ya ce lallai nasara ce da ba zai taba mantawa ba a rayuwarsa ta kwallon kafa da ta kunshi har da lashe kofin duniya a shekarar 1998.

Cikas daya tilo da Zidane ya samu a wannan kaka shine lallasa shi da Man City ta yi a matakin kungiyoyi 16 a gasar zakarun nahiyar Turai.

Zidane ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa sun baiwa lashe kofin Laliga fifiko fiye da komai a wannan kaka.

Kocin ya ce ba zai yanke kaunar cewa wata rana zai horar da babbar tawagar kasar Faransa ba a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.