Wasanni-Kwallon kafa

Yakamata Manchester City ta kori Guardiola- Toure

Tsohon dan wasan Manchester City Yaya Touré.
Tsohon dan wasan Manchester City Yaya Touré. Reuters / Phil Noble

Tsohon Kaftin din kungiyar Manchester City Yaya Toure ya ce lokaci ya yi da za a kori Pep Guardiola da ke horar da kungiyar saboda gazawar da ya yi na lashe kofin zakarun nahiyar Turai da ya yiwa kungiyar alkawari.

Talla

Toure ya ce lashe kofin zakarun nahiyar Turai na daga cikin dalilan da suka saka aka dauko Guardiola a shekarar 2016 amma ganin an kwashe shekara 4 ba tare da kofin ba, lokaci yayi da ya kamata a kawo sauyi domin kawo wani sabon manaja da zai cirewa kungiya kitse a wuta.

Guardiola wanda ya lashe kofin zakarun Turai da kungiyar Barcelona ya gaza samun irin wanna nasara a kungiyar Bayern Munich da kuma Manchester City.

Toure ya ce lokaci ya yi da masu jagorancin kungiyar Manchester City za su yanke hukunci kan abinda su ke so muddin suna bukatar sanya kungiyar cikin jerin manyan kungiyoyin Turai.

Tsohon kaftin din Cote d’Ivoire ya ce kowa ya san Guardiola a matsayin kwararren manaja, amma ganin yadda al’amura suka dakushe masa ya dace a samu sauyi.

Yahya Toure yayi aiki a karkashin Guardiola a kungiyar Barcelona da kuma Manchester City amma kuma sun samu rashin jituwa abinda ya sa Toure ya koma City, kafin daga bisani Guardiola ya koma kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.