Wasanni-Kwallon kafa

Barcelona na son sayen Gini Wijnaldum na Liverpool

Georginio Wijnaldum dan wasan tsakiya na Liverpool.
Georginio Wijnaldum dan wasan tsakiya na Liverpool. Phil Noble/Reuters

Sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Ronald Koeman ya nuna sha’awar sayen dan wasan tsakiya na Liverpool Gini Wijnaldum a kokarin da ya ke na sake fasalta club din wanda ke cike da matsala bayan rashin nasarar lashe La Liga dama wahaltacciyar ficewar da ya yi daga gasar cin kofin zakarun Turai.

Talla

Wasu bayanai sun nuna cewa tuni Koeman ya fara tuntubar Wijnaldum dan Netherlands mai shekaru 29 wanda kwantiraginsa zai kare da Liverpool a shekara mai zuwa.

Sabon Manajan na Barcelona, wanda ya horar da Everton wani lokaci a baya, tsohon dan wasan Neteherlands kuma mai horar da tawagar kungiyar kwallon kafar kasar, ya yi aiki da Gini haka zalika ya bashi horo tun daga yarinta.

A cewar Koeman, Gini da sauran wasu ‘yan wasa da Barcelona ke fatan mallaka za su taimaka matuka wajen kai Club din inda ake fata.

Gini wanda a yanzu farashinsa ya kai yuro miliyan 40, Liverpool na da zabin ko dai ta aminta da sayar da shi a yanzu kan farashi mai sauki ko kuma zuwa karewar kwantiraginsa a badi, ganin yadda bayanai ke cewa dan wasan tsakiyar bai da sha’awar tsawaita kwantiraginsa bisa shawarar Koeman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.