Wasanni-Kwallon kafa

Jami'an tsaron Girka na tsare da Harry Maguire na Manchester United

Harry Maguire dan wasan Ingila da ke taka leda a Manchester United.
Harry Maguire dan wasan Ingila da ke taka leda a Manchester United. Reuters/Ed Sykes

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta ce kaftin dinta Harry Maguire na bada hadin kai ga jami’an tsaron Girka da ya ke tsare hannunsu bayan rikicin da ya faru daren jiya Alhamis a tsibirin Mykonos na Girka.

Talla

Sanarwar da rundunar ‘yansandan Mykonos ta fitar ta ce takaddamar ta faro daga musayar yawu yayinda daga bisani ta kaure zuwa fada har da dukan jami’in dansanda guda, kuma tuni aka kame mutum 3 dukkanninsu ‘yan birtaniya ciki har da Kaftin din na United.

Mai tsaron bayan na Ingila wanda yanzu haka ke hutun karshen kaka a Girka, shi ne mai tsraon baya mafi tsada da aka taba ciniki a tarihin tamaula wanda United ta sayo daga Lesta kan yuro miliyan 80.

Manchester United wadda ba ta yi cikakken bayani kan kamen dan wasanta na ta mai shekaru 27 a shafinta ba, ta ce lamarin ya hada da Maguire da kaninsa da kuma abokinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.