Wasanni-Kwallon kafa

Bayern Munich ta lashe gasar zakarun Turai

'Yan wasan kungiyar kwallon kafa Bayern Munich yayin murnar lashe kofin zakarun Turai a jiya Lahadi.
'Yan wasan kungiyar kwallon kafa Bayern Munich yayin murnar lashe kofin zakarun Turai a jiya Lahadi. Miguel A. Lopes / POOL / AFP

Bayern Munich sun zama zakarun kwallon kafar nahiyar Turai na wannan kaka, bayan doke PSG da ci 1 mai ban haushi a wasan karshe da suka gwabza a daren  Lahadi a birnin Lisbon na kasar Portugal.

Talla

‘Yan wasan Bayern sun kammala kaka mai armashi da wannan nasarar da suka samu, inda suka bar takwarorinsu na Paris Saint Germain da begen kofin da suka fi dauka da mahimmanci.

Dukkannin bangarorin sun buga wasan cikin taka tsantsan amma an dan samu ‘yan damammaki da ba a yi amfani da su ba, kafin a minti na 59 tsohon dan wasan PSG da aka haifa a birnin Paris, Kingsley Coman ya saka kwallo a ragar tsohuwar kungiyar tasa.

PSG za ta ji takaicin baras da damammakin da ta samu a wasu lokuta yayin wasan a filin wasa na Estadio da Luz, mara ‘yan kallo, shi ko kocin Bayern, Hansi Flick, wanda a watan Nuwamba ya maye gurbin Niko Kovac, kakarsa ce ta yanke saka.

Karo na 6 kenan Bayern ta samu wannan kofi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.