Wasanni-Kwallon kafa

An cafke mutane 150 yayin tarzomar magoya bayan PSG

Magoya bayan  PSG a wata arangama da 'yan sanda a birnin Paris a 2013.
Magoya bayan PSG a wata arangama da 'yan sanda a birnin Paris a 2013. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Akalla mutane 150 ne ‘yan sanda suka kama, bayan magoya bayan da kungiyar PSG ta birnin Paris suka kona motoci tare da fasa tagogin shaguna, da kuma arangama da ‘yan sandan Paris sakamakon kasa daga kofin zakarun nahiyar Turai da PSG ta yi.

Talla

‘Yan sandan Paris sun bayyana a shafinsu na Twitter cewa rikicin ya auku ne a kusa da filin wasa na Parc des Princes da kuma titin Champs Elysees yayin wasan da kuma bayan wasan a daren Lahadi.

Dubban magoya bayan PSG ne suka taru a filin wasa na Parc des Princes don nuna goyon baya ga kungiyar ta birnin Paris, amma sai aka doke ta da ci daya mai ban haushi.

An shafe sa’o’i ana wannan rikici, yayin da gungun magoya baya suka yi ta jifar ‘yan sanda da kwalabe da tirtsitsin wuta, su kuma ‘yan sandan suka mayar da martani da harsashen roba da hayaki mai sanya hawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.