Wasanni-Kwallon kafa

Kocin PSG ya yi wa Neymar da Mbappe uzuri

Kocin Paris St Germain, Thomas Tuchel.
Kocin Paris St Germain, Thomas Tuchel. REUTERS/Charles Platiau

Kocin Paris Saint-Germain Thomas Tuchel ya kare ‘yan wasansa biyu da aka kashe Yuro miliyan 400 wajen sayensu, wato Neymar da Kylian Mbappe bayan da suka kasa saka kwallo a ragar Bayern Munich a wasan karshe na zakarun nahiyar Turai da aka doke su 1-0 a jiya Lahadi.

Talla

Masu kungiyar PSG, attajiran nan na kasar Qatar sun kashe Yuro miliyan dari 4 a kan 'yan wasan biyu a shekarar 2017 don kawai su lashe wannan gasa ta nahiyar Turai amma hakan bai samu ba.

Hasali ma, Neymar wanda shi ne dan wasan da ya fi tsada a duniya ya kammala wasan ne da katin gargadi cikin hawaye a maimakon kofin.

Sai dai kocinsa ya kare shi da Mbappe inda ya ce duk da cewa kungiyar na bukatar su ci kwallaye, ba lallai ne a samu haka daga garesu a kullum ba.

Tuchel ya ce ko ma menene, Neymar ya nuna shi gwarzo ne, haka ma Mbappe, wanda bai dade da tashi daga jinyar rauni da ya ji ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.