Wasanni-Kwallon kafa

Pogba zai ci gaba taka wa Man United leda

Dan wasan Manchester United Paul Pogba.
Dan wasan Manchester United Paul Pogba. Reuters

Paul Pogba zai ci gaba da kasancewa a Manchester United a kaka mai zuwa, kuma nan ba da jimawa ba za a fara tattauna batun sabuwar kwantiragi da shi a kungiyar, a cewar wakilinsa.

Talla

Dan wasan mai shekaru 27 da aka saya a kan kudi fam miliyan 89 a shekarar 2016 ya sha fama da jinya, amma ya gwada bajintarsa a wasu wasanni bayan ya dawo, inda kungiyarsa ta kammala kakar gasar firimiya a matsayi na 3.

Wakilin dan wasan Mino Raiola ya ce United ba za ta saurari duk wani mai bukatar sayen dan wasan ba a wannan lokaci.

Raiola ya shaida wa manema labarai cewa Pogba mahimmin dan wasa ne a Man United, kuma yana cikin shirinta na nan gaba.

A kaka mai zuwa ne kwantiragin Pogba zai kare a Manchester United.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.