Wasanni-Kwallon kafa

Sabon dan wasan Barcelona ya harbu da coronavirus

Miralem Pjanic dan wasan da Barcelona ta yi cinikinsa daga Juventus.
Miralem Pjanic dan wasan da Barcelona ta yi cinikinsa daga Juventus. (Photo : Reuters)

Barcelona ta sanar da cewa dan wasan tsakiya da ta saya daga Juventus, Miralem Pjanic ya kamu da cutar coronavirus kamar yadda gwaji ya tabbatar a jiya Lahadi.

Talla

Sanarwa daga kingiyar ta ce dan kasar Bosnian, mai shekaru 30 ba ya tattare da wata kasala, kuma tuni ya killace kansa a gida, tana mai cewa a cikin kwanaki 15 zai yi tataki zuwa Barcelona.

Daga Juventus Pjanic ya koma Barca a wata musanya da kingiyoyin biyu suka yi, inda Barcelonan ta bada dan wasanta, dan kasar Brazil Arthur.

Barca, wacce a karon farko cikin shekaru 12 ta kammala kaka babu ko da kofi guda, za ta fara wasanta na farko a gasar Laligar kakar 2019-20 a ranar 12 ga watan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.