Wasanni-Kwallon kafa

Suarez yana so a fayyace masa matsayinsa a Barcelona

Dan wasan Barcelona  Luis Suarez.
Dan wasan Barcelona Luis Suarez. REUTERS/Albert Gea/File Photo

Luis Suarez ya bukaci shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu ya shaida mai ko baya son aiki da shi a kungiyar.

Talla

Bayan nada Ronald Koeman a matsayin kocin Barcelona, ana sa ran zai gudanar da wasu sauye sauye a tawagar kungiyar, biyo bayan kasa daga Laliga da suka yi, da kuma dukan kawo wuka da suka sha a hannun Bayern Munich da ci 8-2 a wasan daf da kusa da karshe na gasar zakarun nahiyar Turai.

Dan wasan gaban mai shekaru 33 ya ci kwallaye 21 a wasanni 36 da ya buga wa Barcelona a wannan kaka duk da cikas da ya samu sakamakon raunin da ya ji a gwiwa, a shekarar karshe na kwantiraginsa.

Tsohon dan wasan Ajax da Liverpool din ya ce yana so ya ci gaba da murza tamola a Barca, amma kuma zai kyautu a shaida masa idan ba a bukatarsa, duba da yadda ake ta baza jita jitar cewa za a yi waje da wasu manyan ‘yan wasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.