Wasanni-Kwallon kafa

Babu kungiyar da ke shakkar Bayern Munich kafin yanzu- Flick

Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich
Tawagar kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Miguel A. Lopes / POOL / AFP

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich Hansi Flick ya bayyana nasararsu ta dage kofin zakarun Turai a matsayin batu mai cike da al'ajabi ganin yadda a baya kungiyoyin Turai da dama basa ko shakkar haduwa da tawagar tasa duk da kasancewarta babbar kungiya a nahiyar.

Talla

Flick wanda ya yi nasarar kai Bayern ga kofin zakarun Turan karo na 6 baya ga Bundesliga da kuma kofin Jamus duk cikin wannan Kaka, ya ce watanni 10 baya gabanin karbar aikin horar da tawagar ya karanta a jaridu cewa babu kungiyar da ke shakkar Munich.

Cikin watan Nuwamban bara ne Flick ya maye gurbin Niko Kovac don horar da tawagar ta Bayern Munich dai dai lokacin da Club din ke fuskantar tarnaki da rashin nasara, amma kuma zuwansa al’amura suka sauya.

A cewar kocin ko shakka babu Bayern Munich ta cancanci dage kofin na zakarun Turai ganin irin namijin kokarin da ‘yan wasanta ke yi.

Wannan dai ne karo na biyu a tarihin Bayern Munich da ta dage manyan kofunan 3 duk cikin kaka guda.

Nasarar ta ranar Lahadi dai ta nuna cewa baya ga Real Madrid da ta dage kofin zakarun Turan har sau 13 da kuma AC Milan sau 7 babu wata kungiya da ke gaban Bayern Munich a yawan kofunan, sai dai duk da hakan ita ce kungiya 1 a tarihin gasar da ta yi nasara a wasanninta 11 a jere.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.