Wasanni

Maguire na Manchester United zai gurfana gaban Kotun Girka

Harry Maguire mai tsaron bayan Manchester United.
Harry Maguire mai tsaron bayan Manchester United. Pool via REUTERS/Michael Regan

Yau Talata kotu a Girka za ta fara sauraron karar mai tsaron bayan Ingila kuma Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Harry Maguire bayan samunsa da shiga wata hatsaniya da ta kai ga dukan jami’an tsaro a tsibirin Mykonos da ke kasar.

Talla

Yanzu haka dai fitaccen lauya mai kare hakkin bil’adama na Girkan Alexis Anagnostakis shi ne zai kare Maguire a gaban kotu yayin zaman na yau.

Tun a Asabar din da ta gabata ne jami’an tsaro suka saki Maguire da sauran mutum biyun da aka kame ranar Alhamis din da ta gabata, bayanda ya aminta da aikata ba dai dai ba.

Sai dai babbar tuhumar da ke gaban Maguire baya ga tayar da hatsaniyar da kuma dukan jami’in dan sanda bai wuce kokarin bai wa jami’an tsaro cin hanci ba, batun da tuni dan wasan mai shekaru 27 ya amsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.