Wasanni-Kwallon kafa

Messi ya shaida wa Barcelona aniyarsa ta barin kungiyar

Dan wasan Barcelona Lionel Messi
Dan wasan Barcelona Lionel Messi Manu Fernandez/Reuters

Dan wasan Barcelona, Lionel Messi ya shaida wa kungiyarsa a hukumance aniyarsa ta kawo karshen kwantiraginsa da ita kamar yadda wata majiya mai karfi daga kungiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Talla

Lauyoyin dan kasar Argentina din sun sanar da Barca a rubuce bukatar dan wasan nata na barin kungiyar, ta wajen biyan adadin kudin da kwantiragin ya ayyana sai an biya kafin ya yi hannun riga da kungiyar.

Sai dai Barca ta jaddada cewa sai a watan Yunin shekarar 2021 ne kwantiragin shahararren dan wasan zai kare.

Kafafen yada labaran Spain sun ruwaito cewa Messi ya gana da sabon kocin da kungiyar ta dauko, Ronald Koeman a makon da ya gabata, kuma ya bayyana mai cewa ya fi ganin kansa a wata kungiya amma ba Barcelona ba.

Barcelona ta sha mummunar ci 8-2 a hannun Bayern Munich a wasan daf da na kusa da karshe a gasar zakarun nahiyar Turai, lamarin da ya sa aka sallami kocin kungiyar, Quique Setien, da kuma draktan wasannin kungiyar Eric Abidal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.