Wasanni

Makomar Messi bayan raba gari da Barcelona

Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi.
Dan wasan gaba na Barcelona Lionel Messi. Manu Fernandez/Reuters

Masu sharhi kan wasanni na ci gaba da tsokaci kan makomar Lionel Messi na Barcalona da ke son raba gari da Club din na sa bayan shekaru fiye da 16 yana taka leda.

Talla

Akwai dai jita-jitar da ke cewa kungiyoyin kwallon kafa na PSG da Manchester United ne sahun gaba da ke son kulla kwantiragi da dan wasan kuma a shirye suke su biya kudin da ya ke bukata, ko da dai wani batu na daban na cewa Messi na shirin komawa Amurka da taka leda ne don hadewa da David Becham da ya jima yana farautarsa.

Sauran kungiyoyin da masu sharhin ke ganin Messi mai shekaru 33 na iya koma sun hadar da Man City wadda ke yunwar kofin zakarun Turai kuma ta ke da kudin iya sayen dan wasan baya ga haka akwai kyakkyawar alaka tsakanin Pep Guardiola da shi Messi kasancewar ya horar da shi a Barcelona tsawon shekaru.

Haka zalika akwai Inter Milan wadda ke son kawon karshen jan zaren Juventus wadda ta mamaye gasar Serie bayan lashe kofin gasar sau 9 a jere, kuma bugu da kari akwai alaka mai karfi tsakanin Messi da shugaban Club din na Inter Steven Zhang wanda ya ce ya zanta da Messi kan bukatar komawa Club din wani lokaci a baya.

Wasu dai na da ra’ayin cewa Messi ka iya aminta da komawa Italy musamman don bin sahun babban abokin dabinsa Cristiano Ronaldo wanda ya taba kalubalantarsa kan hakan a baya

Yanzu haka dai mahukuntan Barcelona na shirin zaman gaggawa na musamman don tattauna batun na Messi dai dai lokacin da dubban magoya bayan Club din ke gangamin kalubalantar shugabancin Barcelonar tare da neman murabus din shugaban Club din Josep Maria Bartomeu wanda ya ke takun saka da Messi da ake ganin batun ne ya tunzura dan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.