Wasanni

Southgate ya cire sunan Maguire daga tawagar Ingila bayan hukuncin kotu

Harry Maguire mai tsaron bayan Ingila da ke taka leda a Manchester United.
Harry Maguire mai tsaron bayan Ingila da ke taka leda a Manchester United. Reuters/Ed Sykes

Mai horar da kungiyar kwallon kafar Ingila Gareth Southgate ya fitar da sunan Harry Maguire daga cikin tawagar kasar da za ta taka leda a wasannin gasar EURO 2020 bayan zartas masa da hukuncin daurin gidan yari na watanni 21 da kwanaki 10 a shari’ar da ya fuskanta can a tsibirin Syros na kasar Girka.

Talla

Maguire mai tsaron baya mafi tsada da ke taka leda a Manchester United gabanin zartas da hukuncin na jiya yana cikin tawagar da Southgate ya gabatar amma kuma daga bisani ya sanar da janye sunansa bayan dan wasan ya amsa laifinsa tare da karbar hukuncin a gaban alkali.

Hukuncin na Magure mai shekaru 27 na nuna cewa ba wai gidan yari zai shiga ya shafe wa’adin na watanni 21 da kwanaki 10 ba, zai kammala wa’adin nasa ne a waje bisa sanya idanu da sharuddan kotu kuma matukar ya karya koda ka’ida daya ko kuma ya kwatanta aikata irin laifin da aka same shi da aikatawa kai tsaye za a tasa keyarsa zuwa gidan yari.

A cewar Southgate ya janye sunan dan wasan ne da amincewarsa, inda zai daukaka kara kan hukuncin nasa a wata kotu daban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.