Wasanni

Jorge Messi ya soma tattaunawa da Manchester City don kulla yarjejeniya da dansa

Kaftin din Barcelona Lionel Messi tare da mahaifinsa Jorge Horacio Messi daga bayansa, a harabar wata kotun Spain, yayin shari'a kan kudaden haraji. 2/6/2016.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi tare da mahaifinsa Jorge Horacio Messi daga bayansa, a harabar wata kotun Spain, yayin shari'a kan kudaden haraji. 2/6/2016. REUTERS/Albert Gea

Kwararan bayanai daga kafafen yada labaran yankin Catalonia na Spain sun ce Jorge Messi maihaifin kaftin din Barcelona Lionel Messi ya isa Birtaniya, inda tuni ya soma tattaunawa da Manchester City kan sauyin shekar dansa zuwa kungiyar.

Talla

Rahotanni sun ce mahaifin na Messi na tattaunawa da City kan kulla yarjejeniyar shekaru 2, sai dai batun da yafi daukar hankula shi ne kudin da kungiyar ta Manchester City za ta biya.

Messi na ikirarin amfani da wani sashin doka cikin yarjejeniyarsa da Barcelona wajen tilastawa kungiyar bashi damar sauyin sheka a matsayin dan wasa mai zaman kansa, sai dai Barcan tace tun cikin watan Yuni aikin dokar yak are, abinda ke nufin dole ne Messi ko kuma Manchester City su biya kudin sakin dan wasan da ya kai fam miliyan 630.

A bangaren City, wasu majiyoyi daga kungiyar sun ce tana nazarin mikawa Barcelona euro miliyan 150 tare da karin ‘yan wasanta biyu Eric Garcia da Angelino domin sayen Messi, idan ya gaza samun damar sauyin shekar a matsayin dan wasa mai zaman kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.