Wasanni

Messi ya sha alwashin kauracewa atasaye da Barcelona

Lionel Messi
Lionel Messi Manu Fernandez/Pool via REUTERS

A karon farko kaftin din Barcelona Lionel Messi ya shaidawa kungiyarsa cewar zai kauracewa halartar atasaye, kamar yadda sabon daraktan wasannin kungiyar Ramon Planes ya tabbatar.

Talla

Matakin na Messi na zuwa ne bayanda a Talatar da ta gabata ya mikawa shugabannin na Barcelona bukatar rabuwa da kungiyar da ya shafe shekaru akalla 20 tare da ita, bayan daukarsa da ta yi yana da shekaru 13.

Tsamin dangantaka tsakanin Messi da shugabannin Barcelona ya karu ne bayan lallasa sun da Bayern Munich ta yi da kwallaye 8-2 a gasar Zakarun Turai, abinda ya sanya kungiyar gaza lashe ko da kofi guda a tsawon kakar wasa, karo na farko tun bayan shekarar 2007.

Sai dai a gefe daya, magoya bayan Barcelonan masu yawan gaske sun sha alwashin yin iyaka kokarinsu wajen ganin Messi bai sauya sheka ba, wadanda ko a talatar ta da gabata, daruruwansu suka gudanar da zanga-zangar neman shugaban kungiyar Josep Bartomeu yayi murabus.

A cewar fustattun magoya bayan Barcelona Messi shi ne ruhin kungiyar, dan haka muddin babu shi sai dai buzunta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.