Wasanni

Pogba na Manchester United ya kamu da coronavirus

Dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba.
Dan wasan tsakiya na Manchester United, Paul Pogba. Reuters/Lee Smith

Mai horar da tawagar kungiyar kwallon kafar Faransa Didier Deschamps ya ce dan wasansu na tsakiya da ke taka leda a Manchester United Paul Pogba zai rasa damar taka leda a karawar da kasar za ta yi da Sweden ranar Asabar ta sama sakamakon gwajin da ya tabbatar ya harbu da cutar COVID-19.

Talla

A cewar Deschamps yanzu haka Pogba mai shekaru 27 zai kebe kansa ne na tsawon kwanaki 14 kafin sake yi masa gwajin cutar wanda ke nuna cewa zai kuma rasa karawar kasar tasa da Croatia ranar 8 ga watan na Satumba.

Bugu da kari Pogba ba kuma zai samu damar taka leda a wasan farko da Manchester United za ta kara da Crystal Palace ranar 19 ga wata a wasannin sabuwar kaka karkashin gasar Firimiya.

Tuni dai tawagar Manchester United ta aike da sakon fatan samun sauki ga Pogba yayinda tawagar Faransa ta sanar da maye gurbinsa da Eduardo Camavinga dan wasan tsakiyar kasar mai shekaru 17 da ke taka leda a Rennes.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.