Wasanni

Shugaban Barcelona yace zai yi murabus idan Messi ya janye aniyarsa

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu.
Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu. REUTERS/Albert Gea

Shugaban Barcelona Josep Bartomeu yace a shirye yake yayi murabus daga mukaminsa idan kaftin dinsu Lionel Messi ya janye aniyarsa ta rabuwa da kungiyar.

Talla

Tun bayan ficewarsu daga gasar zakarun Turai sakamakon lallasa su da kwallaye 8-2 da Bayern Munich ta yi, tare da neman rabuwa da Barcelona, shugaban kungiyar Bartomeu ke fuskantar suka, inda kwanaki 2 a jere daruruwan magoya bayan kungiyar ke zanga-zangar neman yayi murabus.

Rahotanni sun ce tun bayan gabatar da bukatar sa ta neman rabuwa a ranar talatar da ta gabata, Messi ya daina amsa kiran wayar da shugaban Barcelona Josep Bartomeu ke masa.

Kawo yanzu dai manyan kusoshi 2 da suka hada da tsohon kocinta Quique Setien da daraktan wasanni Eric Abidal Barcelona ta sallama bayan kare kakarwasa ta bana ba tare da cin koda kofi guda ba, karo na farko cikin sama da shekaru 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.