Wasanni

Arsenal ta lashe kofin Community Shield

Pierre-Emerick Aubameyang tare da takwarorinsa na kungiyar Arsenal, yayin murnar lashe kofin gasar Community Shield. 29/8/2020.
Pierre-Emerick Aubameyang tare da takwarorinsa na kungiyar Arsenal, yayin murnar lashe kofin gasar Community Shield. 29/8/2020. Pool via REUTERS/Andrew Couldridge

Arsenal ta lashe kofin gasar tallafawa marasa galihu ta Community Shield, bayan samun nasarar da tayi kan Liverpool a ranar Asabar.

Talla

Wasan da aka fafata a filin wasa na Wembley ya karkare ne a matakin 1-1 bayan mintuna 90, abinda ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron raga, inda Arsenal ta doke Liverpool da kwallaye 5-4.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya ci wa Arsenal kwallon ta tilo Yayin wasan zalika shi ne ya jefa kwallonsu ta biyar a bugun fanaretin da ya basu damar lashe kofin na Community Shield, wanda ake fafatawa Kansa tsakanin kungiyar da ta lashe gasar Firimiyar Ingila da kuma gasar FA.

Gabanin wasan na Community Shield ne dai kocin Arsenal Mikel Arteta ya bayyana kwarin gwiwar cewa Aubameyang zai kara wa’adin yarjejeniyarsa da kungiyar, sabanin fargabar da magoya bayansu ke yi, kan yiwuwar dan wasan ya sauya sheka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.