Wasanni

Lewondoski ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Jamus

Robert Lewandowski dan wasan gaba na kungiya Bayern Munich
Robert Lewandowski dan wasan gaba na kungiya Bayern Munich REUTERS/Michael Dalder

Dan wasan gaba na Bayern Munich, Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Jamus na shekarar bana.

Talla

Lewandowski dan kasar Poland mai shekaru 31 ya lashe kyautar da mujallar wasanni ta Kicker ke bayarwa ne a jiya lahadi, bayan samun kuri’u 276, yayinda takwarorinsa a kungiyarsu ta Bayern Munich Thomas Muller ya samu kuri’u 54, Joshua Kimmich kuma 49.

Jumillar kwallaye 55, Lewandowski ya ciwa Bayern Munich a dukkan wasannin da buga mata a kakar wasa ta bana, inda kuma ya fi kowane dan wasa zura kwallaye a gasa daban daban da ya fafata a bana.

A gasar Bundesliga kwallaye 34 Lewandowski ya ci, 15 a gasar Zakarun Turai, yayinda ya jefa kwallaye 6, a gasar cin kofin Jamus, kuma dukkanin kofunan Kungiyarsa ta Bayern Munich ce ta lashe su.

Nasarorin da dan wasan ya samu ne suka sanya masu sharhi hasashen kyautata zaton shi ne zai lashe kyautar FIFA ta gwarzon duniya a fagen tamaula, bikin karramawar da aka jinkirta saboda annobar coronavirus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.